Yayin da ya ke ganawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hammad al Thani, shugaba Buhari ya ce Najeriya na goyan bayan daukacin kudirorin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su wajen samun kasashe biyu tsakanin Israila da Falasdinu.
Buhari ya shaidawa Sarkin cewar Najeriya za ta hada kai da Qatar har sai ta ga Falasdinu ta samu biyan bukata.
Idan dai ba’a manta ba a shekarar da ta gabata, Najeriya taki kada kuri’ar goyan bayan Falasdinu a kwamitin Sulhu a karkashin shugabancin Goodluck Jonathan.288